Labarai

Ina neman matar Aure – IBB

Tsohon shugaban Najeriya, Janaral Badamasi Badamasi Babangida, IBB mai ritaya, ya bayyana fara neman matar aure.

DABO FM ta tattaro cewa IBB, ya bayyana irin kalar matar da yake so ya aura, ya bayyana cewa duba da irin shekarunshi, yana neman mai tarin shekaru wacce bazata samu matsala donta aureshi ba, haka zalika itama bazata takura ba.

IBB, mai shekaru 78, ya bayyana haka ne a yayin wata ganawa da jaridar SUN, inda ya bayyana tsoron cewa bazai samu wacce zasuyi irin zaman da sukayi da marigayiyar matarshi, Maryam ba.

Maryam Babangida, tsohuwar matar IBB, ta rasu a ranar 27 ga watan Disambar 2009 a wani babban asibitin Jami’ar California dake garin Los Angeles na kasar Amurka.

“Eh lallai da gaske nake. Ina dubawa kuma ina da yakini. Sai dai abin lokaci yana kurewa. Yana (lokaci) cigaba da tafiya, lamarin yana sake shiga matsala.”

“Idan ya kara tsayi, zan tsufa sosai, kuma tunanin samun wata matar auren zai gushe. Amma zanyi kokari in samu kafin lokacin ya zo.”

“Idan akwai wata a kusa, za’a iya hada wa a cikin watanni 3 ko 6. Saboda dole dama sai daga cikin wadanda ka dade da sani ko kuma cikin makusantanka, tinda bazai yiwu kace kawai kana neman aure ba.”

“Duk da haka, zanyi adalci wajen neman matar. Ina matukar son yi adalci. Misali, Bazan nemi yarinya karama wacce na kere mata ba saboda hakan zai zame mana matsala gaba daya.”

“Dole inyi adalci. Abu na biyu shine, Ina tunanin da wacce zan samu ko zamu iya irin zama irin wanda mukayi da Maryam, wanda hakan a yanzu yana da wahala. Ina dai cigaba da addu’a kuma ina tunanin hakan zata kasance.”

Karin Labarai

UA-131299779-2