//
Friday, April 3

Yadda Hakimin Birnin Gwari ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane suna tsaka da barci

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hakimin Birnin Gwari kuma Sarkin Kudun Birnin Gwari Alhaji Yusuf Yahaya Abubakar, wanda aka yi garkuwa da shi kwanaki takwas da suka gabata ya kubuta daga hannun masu garkuwan.

Rahoton mu na nan Dabo FM ya gano hakimin ya kubuta ne a daren ranar Alhamis din daya gabata zuwa wayewar garin Juma’a a wani kauye Sabon Birni inda ake rike da shi.

Duk kuwa da ‘yan uwansa sun biya kudin fansa na Naira miliyan 3.5, amma sun ki sakinsa har sai da Allah ya kubutar da shi ta hanyar guduwa.

Wakilinmu ya ziyarci gidansa da ke a Kaduna inda ya tarar da ‘yan uwa da abokanen arziki cike da suka je  taya shi murna, kamar yadda DailyTrust ta bayyana.

Masu Alaƙa  Duk shifcin-gizo gwamnoni keyi a batun biyan Sabon Albashi -Kungiyar Kwadago

“Allah ne kurum ya kubutar da mu dan haka ina wa Allah  Godiya matuka da Ya sa har na dawo gida lafiya,” in ji shi.

Sarkin Kudun ya kuma ce shi ba zai ce komai ba dangane da halin da ya shiga illa kurum ya mika godiyarsa ga Allah.

Shima wanda aka sace su tare a makon jiya watau tsohon sakataren ilmi a Birnin Gwari watau Ibrahim Musa, shima an ce an sako shi kwana biyu da suka wuce.

Sai dai babu bayanin ko am biya kudin fansa kafin a sake shi.

Mukaddashin Gwamnar jihar Kaduna Aminu Shagali, ya ziyarci gidan Sarkin Kudun, inda ya jajanta masa.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020