Nishadi

Jarumin kasar Indiya yaki kula Ali Nuhu bayan ya tayashi murnar cika shekara 54

A ranar 27 ga watan Disambar 2019, jarumin kasar Indiya, Salman Khan, ya cika shekaru 54 a duniya. Hakan yasa fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Ali Nuhu, ya tayashi murnar zagayowar ranar haihuwarshi.

Ali Nuhu, ya garzaya shafinshi na Instagram domin taya fitaccen jarumin Murna a ranar 27 ga Disamba, inda ya bayyana cewa;

“Ka kasance mai sanya mutane farin ciki. Allah Ya biya ka da wannan Ya kuma yi maka karin nasarori kamar yacce ka kara samu yau. Ina tayaka murnar zagayowar haihuwarka.”

Sai dai DABO FM ta tattaro cewa Jarumi Salman Khan bai yaba da sakon da Ali Nuhu yayi masa ba, hasa lima dai bai kulashi ba.

DABO FM ta tabbatar da rashin ‘Like’, ‘Share’ ko ‘Repost’ da jarumi Salman Khan yaki yi wa jarumi Ali Nuhu.

Wannan ne karo na biyu da jarumawan kasar Indiya suke kin kula ‘Sarki’ Ali Nuhu duk da cewa ana yi masa kallon tauraro a harkar fina-finai ta yammacin Afrika.

A ranar 17 ga watan Agustan 2019, DABO FM ta rawaito yacce jaruma Shraddha Arya tayi kememe ta share ‘Sarki’ Ali Nuhu a sakon tayata murnar cikarta shekara 31, lamarin da ya karyata a wancen lokacin.

Sai dai bayan binciken kafafen labaran Hausa, an samu tabbacin rashin kulashin da jarumar tayi.

UA-131299779-2