Kofin Zakaru: Bayan turnuku da gumurzu, Ronaldo ya fitar da Juventus kunya

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Dan wasan gaba na kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo yayi duk mai yiwuwa wajen fito da kungiyarshi daga zagayen na 16 bayan daya taimaka wajen doke kungiyar Atletico Madrid.

Dan wasan ya jefa kwallaye uku reras a yayin wasan da aka buga a birnin Turin dake kasar ta Italiya.

4CAE9B6F 6531 42B1 8E01 F076FC19EB3C - Dabo FM

Cristiano ya sake kafa wani tarihi akan kungiyar ta atletico, domin kuwa shine dan wasa na karshe daya jefawa Juventus kwallo uku a raga. Ya jefa a shekarar 2012, 2014, 2017 da kuma 2018.

FAEB8374 A47F 4E7E B857 15492537580A - Dabo FM

Yanzu dai kungiyar ta Juventus zata tafi mataki na gaba a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

Dan wasan yayi wannan bajintane a daidai lokacin da tsohuwar kungiyarshi ta Real Madrid tasha kayi a gasar ta nahiyar turai, lamarin da yayi sanadiyyar ficewarta daga gasar bayan da kungiyar Ajax ta doke ta da ci 4-1 a filin Santiago Bernabeu dake birnin kasar Spaniya.

 

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00