Ko Abba zai zamo mafi alkhairi a Kano, Allah kada ka bashi nasara – Usman Liti

Wani matashi mai suna Usman Shehu Liti   ya roki Allah ya hana dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jami’iyyar PDP mulki, sai dai nashi salon yazo da ganganci tare da shiga hurumin mahalicci, inda yace ko da shine alkhairi, Allah kar ya bashi nasara.

Sai dai munji kokarin jin ta bakinshi domin yayi karin haske ko bayyana dalilan dayasa yayi wannan kalami amma bai bamu amsawa ba har kawo yanzu da muke hada wannan rahoto.

 

 

Kalaman na Usman sun janyo cece kuce a shafinan sada zumunta, inda wasu suke kallon hakan da rashin wayewa ta fuskar addini dama zamantakewar rayuwa, duba da hadisin da shugaban tsira yace “Ka fadi alkhairi ko kayi shiru.”

Masu Alaƙa  Saurayi ya kashe kanshi bayan zargin fyade

Mene ra’ayinku game da wannan?

Zaku iya bayyana a shafinmu na facebook, Dabo FM

Muhammad Aliyu Dangalan

•Sublime of Fagge's origin. •Apprentice Journalist. •Doctor of Pharmacy student.


Warning: file_put_contents(/var/www/u0619820/data/www/dabofm.com/): failed to open stream: Is a directory in /var/www/u0619820/data/www/dabofm.com/wp-content/plugins/propellerads-official/includes/class-propeller-ads-anti-adblock.php on line 203
%d bloggers like this: