Sojoji sun tseratar da mutum 760 da akayi garkuwa dasu, sun kashe ‘yan bindiga 55 a Zamfara

Karatun minti 1

Rundunar sojin Najeriya reshen jihar Zamfara ta hallata ‘yan bindiga masu tada zaune tsaye guda 55, ta kuma tseratar da mutane kimamin 760 daga masu sace mutane.

Rundunar ta bayyana hakan a wata takarda data aikewa manema labarai daga Major Clement Abiade jiya Talata a birnin Gusau dake jihar Zamfara.

Major Clement yace rundunar ta samu nasarar kwace makaman ‘yan bindigar tare da  kose duk wata kafa da zata basu damar ficewa daga dagin a lokacin da sukayi musu kawanya.

Jaridar Leadership ta rawaito cewa rundunar ta kwace bindiga kirar AK-47 guda 4, Bindigar Rocket Propelled guda 1, Bindigar Dane guda 12, kwanson harshashin AK-47 guda 27, harshashai 168 hadi da babura 47, mota kirar Golf Wagon tare da bangararrun shanu guda 61.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Latest from Blog