(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kotu ta bada belin Sanata Abbo akan kudi Naira miliyan 5

Karatun minti 1

Rundunar yan sanda mai kula da shiyyar Abuja ta maka Sanata Elisha Abbo mai wakiltar yankin arewacin jihar Adamawa, zuwa kotu bayan da aka zarge shi da cin zarafin wata mata a wai shagon siyar da kayyakin tada sha’awar dan adam.

Faifan bidiyon da aka hangi Sanatan yana mammake matar a shagon dai ya karade kafafen sadarwar Najeriya baki daya.

DABO FM ta binciko cewa tin a kwanakin da lamarin ya faru, Sanata Abbo ya nemi gafara akan abinda ya aikata.

Sai dai DAILY TRUST ta rawaito cewa a ranar Litinin, Sanata Abbo ya musanta zargi da akeyi masa a gaban kotu na cin zarafin tare da aikata mummunan laifi.

Sai dai ya roki kotu data yi masa afuwa inda mai shari’a, Abdullahi Ilellah, ya ayyana Naira miliyan 5 a matsayin kudin belin Sanata Abbo.
Kotun ta dage zamanta zuwa 28 ga watan Julin shekarar 2019.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog