Labarai

Budurwa ta rasa ran ta bayan amfani da ‘Maganin kashe kwari’ don cire kwarkwata

Sashin Hausa na Legit ya rawaito cewa; Wata matashiya, Ayomikun Juliana, da ke bautar kasa (NYSC) a garin Osogbo, babban birnin jihar Osun, ta mutu bayan an yi zargin ta shafa maganin kashe kwari mai karfin gaske (Sniper) a kan ta domin ta kashe kwarkwatar da ta dame ta.

Matashiyar ta je shagon gyaran gashi, inda aka gano cewa akwai kwarkwata a cikin gashin kan ta. Bayan ta dawo gida, sai ta yanke shawarar yin amfani da ‘sniper’ domin ta kashe kwarkwatar.

Matashiyar ta shafa maganin kashe kwarin kafin ta kwanta tare da yin amfani da hula ta rufe kan ta. Amma da safe sai aka same ta a sankame, kamar ta suma. An garzaya da ita zuwa asibiti domin ceto ran ta amma daga bisani ta ce ‘ga garinku nan’.

Karin Labarai

Masu Alaka

Budurwa ta caccakawa Saurayinta na daduro wuka a jihar Legas

Dabo Online

‘Ungozoma’ ta yanke wa mijinta Harshe da Hanci, ta kira Surukarta ta dauki gawa

Dabo Online

Budurwar Zamfara da ta kona kanta tana samun kayatattun kyaututtuka da tallafin Kudade

Dabo Online

Uwargida ta caccakawa Mijinta wuka a jihar Kaduna

Dabo Online

Wata Mata ta kwararawa Saurayin diyarta ruwan zafi a gadon baya

Dabo Online
UA-131299779-2