An bukaci al’umma su saka fitaccen jarumi Sani Idris ‘Moda’ a addu’o’in bisa matsananciyar rashin lafiya

Karatun minti 1

Al’umma daban daban musamman ma’abota kallon fina finan Hausa, sun bukaci musulmai da su saka fitaccen jarumi ‘Moda’ a cikin addu’o’in na yau da kullin.

DABO FM ta binciko cewa tin dai a makon da muke ciki ne dai aka yankewa Sani Idris (MODA) kafarshi ta hagu.

Binciken da muka gudanar ya bayyana cewa jarumi Sani Idris Moda, yana fama ne da cutar siga kamar yacce jaruma Saratu Gidado Daso ta bayyana a shafinta Instagram.

Yanzu haka dai jarumin yana kwance a asibiti domin cigaba da karbar kulawa daga hannun likitoci.

Al’umma da dama sunyi kira da a saka jarumin a cikin addu’o’i domin samun sauki.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog