Labarai

Ku daina kara kudi a kayayyakin masarufi dan Allah- Shugaban manoma ga ‘yan kasuwa

A dai-dai lokacin da ake kukan tsadar rayuwa saboda sanya dokar takaita zirga-zirgar jama’a da ababen hawa a sassan kasar nan, an bukaci ‘yan kasuwa musamman masu sayar da hatsi da su yi wa Allah su daina kara farashin kayayyakin masarufi saboda yanayin da aka shiga a kasar nan.

Shugaban kungiyar manoma da safarar hatsi ta kasa, Alhaji Haruna Ahmad Panbeguwa ya bayyana hakan, sa’ilin zantawarshi da Dabo FM a Zariya.

Ya kwatanta halin da ake cikin a matsayin wani jarabi daga Allah madaukakin Sarki, kana ya nuna bakin cikinshi kan yadda wasu ke amfani da wannan lokaci wurin tsawwalawa mabukata da marasa karfi duk da halin kunci da al’umma ke ciki.

Ya kara da cewa, ba yanzu ne karo na farko da ake samun annoba ba, ko zamanin annabawan Allah da sahabbai an samu jarabi ta annoba. Sannan ya yi fatan samo maganinta nan bada jimawa ba.

Da ya juya ga bangaren gwamnati kuwa, Alhaji Haruna Ahmad Panbeguwa, ya naimi ganin ta wadata al’ummar ta ne da kayayyakin more rayuwa da zai inganta jin dadin su, sannan ya yaba ma shirin gwamnati na ciyar da mabukata a irin wannan lokaci.

Ya tabbatar da aniyar kungiyar su na raba kayan masarufi kyauta ga marasa galihu, kuma ya naimi membobin kungiyarshi kan su cigaba da girmama umarnin gwamnati domin samar da tsari mai kyau.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kwabid-19: Ya kamata gwamnati ta bari koda mutane 12 su yi Sallar Juma’a-Sheikh Comasi

Mu’azu A. Albarkawa
UA-131299779-2