0

Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 12 da ranar yau Talata.
Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 151.
“A yau da misalin karfe 12:30 na rana an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 12. An samu guda 9 a Osun, 2 a Edo, 1 a Ekiti.”
Ga jerin adadin da aka tabbatar a kowacce jiha;
- Lagos – 81
- Abuja – 25
- Ogun – 4
- Inugu – 2
- Ekiti – 2
- Oyo – 8
- Edo – 4
- Bauchi – 2
- Osun – 14
- Rivers – 1
- Binuwai – 1
- Kaduna – 3

