Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 23 a daren Laraba.
Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 174.
“A yau da misalin karfe 08:00 na dare an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 23. An samu guda 9 a Lagos, 7 a Abuja, 5 a Akwa Ibom 1 a Bauchi da Kaduna.”
Ga jerin adadin da aka tabbatar a kowacce jiha;
Lagos – 91
Abuja – 35
Ogun – 4
Inugu – 2
Ekiti – 2
Oyo – 8
Edo – 4
Bauchi – 3
Osun – 14
Rivers – 1
Binuwai – 1
Kaduna – 4
Twenty-three new cases of #COVID19 have been reported in Nigeria; 9 in Lagos, 7 in the FCT, 5 in Akwa Ibom, 1 in Kaduna and 1 in Bauchi State
As at 08:00 pm 1st April there are 174 confirmed cases of #COVID19 reported in Nigeria. Nine have been discharged with two deaths pic.twitter.com/Wy9MzX1lsr