Home LabaraiKungiyar masu sarrafa Shinkafa zasu fara siyar da kowanne buhu akan N13,300

Kungiyar masu sarrafa Shinkafa zasu fara siyar da kowanne buhu akan N13,300

by Dabo Online
0 comments

Kungiyar masu sarrafa Shinkafa a Najeriya ‘RIPAN’ ta aminta da fara siyar da buhun shinkafa akan Naira 13,000 kowanne buhu.

Kungiyar ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Agustar shekarar 2019, ta hannun shugabanta, Muhammad Maifanta.

Kungiyar ta yabawa shugaba Muhammadu Buhari bisa umarnin rufe iyakokin Najeriya musamman na kasar Benin, inda ake yawan kwaranyo Shinkafa zuwa Najeriya.

DABO FM ta tattaro cewa Shugaban kuniyar, Maifanta, ya bayyana cewa “Baza muyi amfani da rufe iyakoki wajen kara farashin Shinkafar ba.”

“Dukkaninmu, mun amince zamu siyarda Shinkafa kowanne buhu akan N13,300 mafi karanci, sai dai duba da nisan was masu siyarda Shinkafa farashin zai iya karuwa.”

“Amma duk da haka, babu wani wata Shinkafa a Najeriya da za’a siyar da ita sama da N14,000 kowanne buhu.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00