Labarai

Mallam Shekarau ya caccaki gwamnan Ribas akan rushe Masallaci

Tsohon gwamnan jihar kuma Sanatan Kano ta tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau, ya soki lamirin rushe Masallaci da gwamnan jihar Ribas yayi a makonni da suka gabata.

DABO FM ta binciko wata takarda mai dauke da sa hannun Mallam Shekarau, wacce aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis, 29 ga watan Agustar 2019.

“Ya kamata dukkanin ‘yan kishin kasa su hadu wajen sukar lamirin abinda gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya aikata na ruguje ‘Babban Masallacin Rainbow Town’ dake unguwar Trans-Amadi a garin Fatakwal ta jihar Ribas, babu gaira babu dalili, hadi da tabbatar da jihar ta Ribas a matsayin jiha ta addinin Kiristanci tare da yin ikirarin cewa ba’a neman afuwar kowa.”

Mallam Shekarau yayi kiran cewa dukkanin “al’ummar musulmin kasa baki daya yakamata suyi Allah wadai da aikin wautar da gwamnan yayi, domin burin gwamnan shine ya haddasa fatan addinin da ba’a taba ganin irinshi ba.”

“In da ace wani gwamnan jihar Musulmai ne ya fito ya tabbatar da jiharshi a matsayin ta musulmai, kuma ya tunkari rushe Cocina babu gaira babu dalili, da tini anyi masa caa, bangaren shugabanci Kiristanci zai mika kokenshi ga Majalissar Dinkin Duniya, da suna nan suna bukatar kariya daga kangin musulunci.”

“Babu wata kwakwalwa mai tunani da zatayi tunanin aikata abinda gwamna Wike yayi a kasar da take cike da addinai da al’adu wadanda suka hadu suka samar da Najeriya.”

Mallam Shekarau ya kara da cewa; “Muna kara maimatawa cewa “Idan da musulmi ne ya aikata rabin abinda Wike ya aikata, ta tini kasar tayi wani bangare na barazana da zaman lafiyarta. Amma muna nan gashi duk malaman Kiristancin suna goyon bayan abinda ya aikata.”

DABO FM ta tattaro Mallam Shekarau, inda ya kara da cewa; “Najeriya dai ta kowa ce, kuma babu wata jiha da zata mayar da kanta ta mabiya addini guda daya. Fahimtar mulki ce take sawa a ayi shugabancin da za’a bawa kowa hakkinshi.”

“A lokacin da nayi gwamnan Kano daga shekarar 2003 zuwa 2011, mun dora mutane akan domin suyi rayuwarsu bisa Shari’ar Musulunci, amma giyar mulki bata ja mu mu fara rushe Cocina da hana kowa yin addininshi ba.”

“Munyi adalci ga kowanne bangaren addini wanda hakan tasa muka samu lambar yabi daga Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kano dama ta kasa baki daya.”

Ya kara da cewa; “Har yanzu wadannan malaman Kiristancin suna raye kuma zasu iya tabbatar da abinda nake fada.”

“Abin zai iya baiwa Wike sha’awa kan cewa, acikin gwamnati na akwai Kiristocin da na dauka a matsayin masu bani shawara (Mista Tara Illo da Mista Chris Chubuzor Azuka).

“Karyar Wike taci karya da yace jihar Ribas jiha ce ta Kiristoci. Kiristocin jihar Ribas basu da kaso 100 na mutanen jihar ba, akwai Musulmai da sauran mabiya wasu addinan.”

“Kuma yana nufin yace jihar Ribas tana tafiyar da gwamnatin ta ne daban da abinda Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Kudaden da ake bamu ‘basu taka kara sun karya ba’ – Sanata Shekarau

Raihana Musa

Zaben Gwamna: Mal Shekarau yasha kayi a akwatin kofar gidanshi

Abuja: Malam Shekarau ya karbi shedar zama sanatan Kano ta Tsakiya daga INEC

Ina tsoron karawa da Kwankwaso – Shekarau

Dabo Online

Nayi rantsuwa da nufin isar da aikenku, zan sauke nauyinku da sahalewar Allah – Dr Shekarau

Dabo Online

Shekarau ya kammala kada kuri’arshi a zaben shugaban majalissar Dattijai

Dabo Online
UA-131299779-2