Labarai

Kwankwaso yayi Allah wadai da cigaba da tsare Dadiyata da matsalolin sace-sacen Mutane

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Dr Rabi’u Kwankwaso, ya Allah wadai da kamun da cigaba da tsare dan gwagwarmayar nan, Abubakar Idris Dadiyata.

Kwankwaso ya kuma nuna takaici da bakin cikin kan yacce tabar-barewar sace-sacen mutane ta zama ruwan dare a jihohin Arewacin Najeriya.

DABO FM ta binciko cewa Kwankwaso ya bayyana haka ne a wani sako daya wallafa a shafinshi na Twitter.

Kwankwaso yayi tsokaci akan harin da ‘yan Bindiga suka kai jihar Katsina wanda yayi sanadin garkuwa da mutane sama da 50 wadanda akasarinsu Mata ne da kananan Yara.

“Abin damuwa ne da takaici kan yacce ayyukan sace-sacen mutane da hare-hare yayi yawa a ‘yan watannin nan.”

A ‘yan kwanakin da suka gabata, akayi garkuwa da daliban Jami’ar Ahmadu Bello Zaria tare da sace mutane 50 wadanda akasarinsu Mata ne da Kananan Yara a makon daya gabata a jihar Katsina.”

Kwankwaso, yayi karin haske tare da bayyana cewa sunyi dukkanin iya kokarinsu wajen gano inda matashi Abubakar Dadiyata yake, amma abin yaci tura.

“Yau kwanaki 27, amma har yanzu bamu samu wani rahota daga rundunar ‘yan sanda da sauran Jami’an tsaro ba.”

DABO FM ta tattaro Kwankwaso yana cewa sunyi kokari don gano hakikanin abinda ya faru da Dadiyata, inma anyi garkuwa dashi ne ko kuma an tsare shi ne, “Dukkanin kokarinmu, hakarmu bata cimma ruwa ba.”

Daga karshe yayi kira ga jami’an tsaro da kada su manta cewa;

“Wajibi ne akan jami’an Tsaro da su tsare rayuwar dukkanin wani dan kasa tare da gudar tauye hakkokin da kasa take baiwa kowa.”

Tin dai 3 ga watan Agusta 2019, aka dauke matashi , Abubakar Idris Dadiyata, a gidanshi dake jihar Kaduna.

Karin Labarai

Masu Alaka

Sandar da Sabbin Sarakunan Kano suke rikewa “Kokara” ce – Kwankwaso

Dabo Online

Dama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Yadda Ganduje ya taka rawa a taron kaddamar sabon garejin gyaran motoci na mata da maza

Dabo Online

Kwankwaso ya nuna takaici da bakin ciki akan kashe-kashe da sace-sacen Mutanen Arewa

Dabo Online

Zaben Kano shine ma’aunin darajar INEC – Kwankwaso

Arewa nada bukatar Jagororin irin Kwankwaso – Sheikh Ibrahim Khalil

UA-131299779-2