Al'aduLabaraiTaskar Matasa

Daliban Kano sun lashe gasar Kwalliyar Gargajiya ta Jami’ar ABU bayan sunyi ado da Jajayen Huluna

Daliban jihar Kano dake karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, sun samu nasarar lashe zaben jihar da ta fi kowacce jiha iya kwalliyar Gargajiya.

An gudanar da zaben ne bayan anyi shagulgulan raya al’adun Najeriya na shekarar 2019 mai taken ‘ABU Grand Cultural Carnival 2019.

Kano ta dai samu nasarar lashe gasar ne bayan an jefa kuri’u 7,131 a shafin Twitter, inda Kano ta doke takwarta ta jihar Borno.

A kason kuri’un, kowacce jiha ta samu kaso 50 bisa dari, sai dai jihar Kano tayi zarra ne da yawan kuri’u wanda iya masu lura da shafin ne zasu iya ganin adadin kuri’ar da kowacce jiha ta samu.

Jihohi dayawa ne suka fafata, sai dai jihar Borno da Kano ne suka kai zagayen karshe.

Ga wasu daga cikin Hotunan jihohin;

Kano

Borno