//
Wednesday, April 1

Kwankwaso ya nuna takaici da bakin ciki akan kashe-kashe da sace-sacen Mutanen Arewa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Dr Rabi’u Kwankwaso yayi Allah wadai tare da nuna takaici da bakin cikin kan yacce tabar-barewar sace-sacen mutane da yin garkuwa da su ya zama ruwan dare a jihohin Arewacin Najeriya.

DABO FM ta tattaro cewa Kwankwaso, Ya kumayi Allah wadai da kamu da kuma cigaba da tsare dan gwagwarmayar nan, Abubakar Idris Dadiyata.

DABO FM ta binciko cewa Kwankwaso ya bayyana haka ne a wani sako daya wallafa a shafinshi na Twitter.

Kwankwaso yayi tsokaci akan harin da ‘yan Bindiga suka kai jihar Katsina wanda yayi sanadin garkuwa da mutane sama da 50 wadanda akasarinsu Mata ne da kananan Yara.

“Abin damuwa ne da takaici kan yacce ayyukan sace-sacen mutane da hare-hare yayi yawa a ‘yan watannin nan.”

Masu Alaƙa  ‘Yan sanda sunyi alkawarin kama duk masu hannu a yiwa Pantami ihun ‘Bamayi’

A ‘yan kwanakin da suka gabata, akayi garkuwa da daliban Jami’ar Ahmadu Bello Zaria tare da sace mutane 50 wadanda akasarinsu Mata ne da Kananan Yara a makon daya gabata a jihar Katsina.”

Kwankwaso, yayi karin haske tare da bayyana cewa sunyi dukkanin iya kokarinsu wajen gano inda matashi Abubakar Dadiyata yake, amma abin yaci tura.

“Yau kwanaki 27, amma har yanzu bamu samu wani rahota daga rundunar ‘yan sanda da sauran Jami’an tsaro ba.”

DABO FM ta tattaro Kwankwaso yana cewa sunyi kokari don gano hakikanin abinda ya faru da Dadiyata, inma anyi garkuwa dashi ne ko kuma an tsare shi ne, “Dukkanin kokarinmu, hakarmu bata cimma ruwa ba.”

Masu Alaƙa  Kwankwaso bashida takardun kammala Firamare - Ganduje

Daga karshe yayi kira ga jami’an tsaro da kada su manta cewa;

“Wajibi ne akan jami’an Tsaro da su tsare rayuwar dukkanin wani dan kasa tare da gudar tauye hakkokin da kasa take baiwa kowa.”

Tin dai 3 ga watan Agusta 2019, aka dauke matashi , Abubakar Idris Dadiyata, a gidanshi dake jihar Kaduna.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020