(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ma’aikatan Cross River sun nuna rashin jin dadi bisa yacce Gwamnan jihar ya albashi 1 ga wata

Karatun minti 1

Ma’aikatan jihar Cross Rivers sun koka kan yadda Gwamnan jihar Ben Ayade ya biya albashi ranar 1 ga watan Mayu.

Gwamana Ben Ayade ya kasance yakan biya albashi a farkon sati na wata a cikin wa’adin mulkinshi na shekara 3, duk da ba koda yaushe ba.

Ya yakewa manema labarai jawabi, shugaban Trader Union COngress, Clarkson Otu, yace ma’aikatan jihar basu ji dadi kan biyan albashin da gwamnan yayi a farkon wata ba.

Yace duk da dai gwamnatin tana aiki tukuru, ma’aikatan basa jin dadin biyan kudin a farkon wata.

“Baya goyon bayan biyan albashi a frkon wata. Mun fadawa Gwamna cewa yin hakan bai dace ba. Sati 1 daya wuce aka biyamu albashin watan Afrilu, yanzu kuma 1 ga wata ya biyamu na watan Mayu.”

“Duk da irin zanga-zanga da mukeyi na nuna rashin jin dadi, abin da mamaki ace har yanzu gwamna bai dena ba.”

Duk da jihar Cross River na daga cikin jihohin da suke da mafi karancin kudaden shiga daga gwamntin tarayya, jihar ta kasance jiha ta ukun karshe a jerin jihohi masu cin bashi a Najeriya, a bangare guda kuma Gwamna ya kasance mai rashin wasa kan biyan albashin ma’aikata a jihar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog