‘Yan Bindiga sun sace surukin babban Dogari ‘ADC’ ga shugaba Buhari

A yau Laraba, Masu garkuwa da mutane sukayi wa garin Daura na jihar Katsina kwawanya, wanda ya kai su ga sace Magajin Garin Daura, Musa Umar a gidanshi dake garin na Daura.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa an dauke Musa Umar bayan ya idar da sallar Magariba a garin na Daura.

Magajin Garin na Daura shine Mahaifin Fatima Musa, uwar gidan Colonel Mohammed Abubakar, babban dogarin ”ADC” shugaba Muhammadu Buhari

Daily NIGERIAN ta hada bayanan da yace ‘yan bindigar sunyi ta harbe harbe domin tarwatsa mutane inda sukayi amfani da hakan suka sace shi a cikin mota Peugeout kirar 406.

Sauran LAbarin na zuwa….

Masu Alaƙa  Zamfara: 'Yan Bindiga sun afka makarantar Sakandire ta 'Yan Mata, sun sace mutane da dama

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.