Mai tsaron raga, Iker Casillas ya kamu da ciwon Zuciya

Karatun minti 1

Mai tsaron ragar kungiyar kwallFC Porto dake kasar Portugal, Iker Casillas uya kamu da ciwon zuciya a safiyar yau kamar yadda club din ya bayyana.

Tsohon dan wasan Real Madrid mai shekaru 37 dai yanzu haka yana Asibiti domin karbar kulawa kamar yadda Jaridar A Bola ta kasar Portugal ta bayyana.

Jaridar tace ciwon ya kama Casillas ne dai dai lokacin da mai horas wa na kungiyar, Sergio Conceicao, yake baiwa yan wasa atisaye a yau Laraba.

Casillas ya baro kungiyar Real MAdrid zuwa Fc Porto tin a shekarar 2015, ya samu nasarar lashe gasar La Liga sau 5, Kofin Zakarun Turai 3, Copa del Ray 2 a wasanni 725 daya bugawa kungiyar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog