Labarai

Maigatari, Daura da Jibiya na daga cikin garuruwan da aka haramta sayar da man fetir

Ma’aikatar lura da arzikin man fetur wato DPR ta daina ba da damar gina gidan mai tare da janye ba da lasisi ga gidajen mai dake da kusancin kilomita 20 da iyakokin Nijeriya har lokacin da Allah ya so.

Jaridar Daily Trust ta ba da rahoton cewa, hukumar ta alamta hakan ga masu bukatar gina sabbin gidajen mai a yankunan.

DPR ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta yanke wannan shawara shi ne, taimakawa muradun gwamnati na hana fasa kwaurin man fetur a iyakokin kasar.

Kakakin hukumar DPR, Paul Osu, ya ce: “Bisa ga wannan sanarwa, muna bai wa dukkan wuraren ajiye man fetur da ‘yan kasuwar mai shawarar su daina kai man fetur wuraren har sai sun sake tuntubarsu.”

Wannan ya biyo bayan umurnin hukumar hana fasa kwauri wato Kwastam, inda ta hana sayarwa gidajen mai dake kimanin kilomita 20 da iyakokin Nijeriya man fetur.

Ga dai jerin garuruwan dake kusa da iyakokin Nijeriya uku da wannan abin zai shafa:

  1. Gamboru Ngala – Jihar Borno

2. Mubi – Jihar Adamawa

3. Garin-gada, Yunusari LGA Maigatari – Jihar Jigawa

4. Daura – Jihar Katsina

5. Jibiya – Jihar Katsina

6. Illela – Jihar Sokoto

7. Ilo, Tsamiya, Bagugu – Jihar Kebbi

8. Kamba – Jihar Kebbi

9. Idiroko – Jihar Ogun

10. Seme – Jihar Legas

Karin Labarai

UA-131299779-2