Sabon bincike ya nuna cewa yaren Hausa da akafi yi a Arewacin Najeriya da wasu kasashen Afirka irinsu Kamaru, Nijar, da Chadi ce yare ta 11 a duniya.
A cewar Spectator Index, bincike ya nuna cewa mutane milyan 150 ke amfani da harshen Hausa a duniya, kuma tafi yaren Indiya da Jamus shahara.
Yarin yan kasar Sin, Mandarin, ne yare mafi yawan amsuwa da kuma yi a duniya, sannan sai yaren Turanci mai mutane milyan 983.
Ga jerin:
1- Yaren Mandarin: Mutane biliyan 1,090
2- Turanci: Mutane milyan 983
3- Hindustani: 544
4- Yaren Andalus: 527
5- Larabci: 422
6- Malay: 281
7- Yaren Rasha: 267
8- Bengali: 261
9- Yaren Fotugal: 229
10- Yaren Faransa: 229
11- Hausa: 150
12- Punjabi: 148
13- Yaren Jamus: 129
14- Yaren Yabaan: 129
15- Yaren Farisa: 121
16- Swahili: 107 T
17- Telugu: 92
