(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Manoman Shinkafa 1,108 a Daura, zasu amfana da bashin Noma a Daura daga shugaba Buhari

Karatun minti 1

Manoma 1,108 yan asalin garin Daura ne zasu amfana da shirin bashin manoma da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kirkiro.

Shirin Noman Damuna kashi na daya na shekarar 2019.

Shugaba shiyyar Kungiyar Manoman Shinkafa, RIFAN, ta jihar Katsina ya bayyana haka ne a wata ganawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ranar Juma’a a garin na Daura.

Yace zuwa yanzu an kammala shire-shiryen raba kayayyakin noman ga wadanda suka samu shika cikin shirin wadanda suka cimma dukkan abinda aka bukata.

Yace kowanne manoma zai amfana da Injin janyo ruwa, taki, maganin kwari, maganin hana girman shuka, da iri a matsayin bashi, wanda zasu biya da Shinkafa ta cikin kwanso a cikin shekara 1.

Mr Bature ya kara bayyana cewa a shirin da za’a gudanar na biyu, zasu yi kokarin daukar mutane 5,800 a watan Yuli.

Kamfanin dillancin Labaran Najeriya ya rawaito cewa kusan mutane 2,500 ne suka amfana tin farkon fara shirin a shekaru 3 da suka wuce.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog