Dokar baiwa kananan hukumomi ‘yancinsu zata fara aiki 1 ga watan Yulin 2019

Biyo bayan dauki ba dadi da akayi ta fama wajen kokarin cire ikon kananan hukumomi daga wajen gwamnoni da shugaba Muhammadu Buhari yake kokarin yi.

Kungiyar Gwamnonin sun aminta da shirin a wani taro karawa juna sani da kwamitin tabbatar da shirin ya shirya a Otal din Transcorp dake birnin tarayyar Abuja a jiya Alhamis.

Majiyoyin DaboFM sun rawaito cewa, shugaban kungiyar gwamnonin, ABdulaziz Yari na jihar Zamfara wanda ya samu wakilcin Muhammad Abubakar na jihar Bauchi ya bayyana amintar kungiyar na baiwa kananan hukumomi damar cin gashin kansu.

“Na amince da bukatar shugaba Buhari na ganin bangaren sharia da kananan hukumomi sun samu yancin cin gashin kansu idan har ana bukatar Dimukradiyyarmu ta daure, hakan zai kara kaimi, sahihanci da kuma tsantseni a harkar gwamnati.” – Yari

Masu Alaƙa  Gwamnoni sun roki Buhari ya cire dokar bai wa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye

Shima a nashi jawabin, mataimakin shugaban majalissar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ya yaba da wannan tsari inda ya bukaci a karfafawa kananan hukumomin tare da yiwa dokokinsu garanbawul.

A makonnin da suka gabata dai , gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana nan a kan bakarta na aiwatar da shirin daga ranar 1 ga watan Yuli shekarar 2019.

Alkalan Alkalai na jiha 34, shugabannin majalissun jihohi 31, Gwamnoni masu yawa ne suka samu halartar taron.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.