Ku taimaka, ku daina cin Shinkafa ‘yar kasar waje, tana dauke da Guba – Shugaban Custom

dakikun karantawa

Shugaban Hukumar hana fasa kwauri ta CUSTOM, Hameed Ali, ya bayyana cewa shinkafar da ake shigo da ita daga kasahen ketare ba tada kyau, hasalima akwai guba a cikin ta.

Shugaban dai yace dukkanin wata Shinkafa yar kasar waje da aka ganin a cikin kasa Najeriya, to lallai fasa kaurinta akayi.

Yayi kira ga al’ummar Najeriya da su kauracewa siyan Shinkafa ‘yar kasar waje saboda ta haka ne za’a hana masu yin fasa kaurin shinkafa ci gaba da yin haramtacciyar sana’ar da hukumar ta hana.

Kamfanin dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya rawaito cewa, Hameed Ali ya bayyana haka ne a wani taron karawa juna sani da ma’aikatar kudin Najeriya ta shirya a jiya  Alhamis a babban birnin tarayyar Abuja.

Hameed Ali yace gwamnatin tarayya bata bawa kowa lasisin shigowa da Shinkafa ba, kuma ya bada tabbacin cewa duk Shinkafar da aka ganta a gari, to babu shakka, fasakaurinta akayi.

Yace Shinkafar da ake shigowa da ita kasar tana shafa kusan shekaru 5 a ajiye, wanda yace ya tabbata akwai wasu sinadarai da suke lalata ingancinta.

Ya bayyana cewa yawancin wa’adin amfani dasu yak are, amma sai a chanza buhu a cigaba da siyarwa da mutane, wanda kuma haka yana kawo cututtuka.

“Ina kira ga al’ummar Najeriya da su taimaka su rungumi shinkafar mu ta gida, tana nan ana siyarwa, tafi dauke da sinadaran lafiya, idan kukayi haka to lallai zaku taimakawa hukumar Custom wajen yaki da masu fasakauri.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog