(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Mata ta ke bukatar kudin asibitin, in ji magidancin da ya siyar da jaririnsa

Karatun minti 1

Rundunar ‘yan sanda Najeriya a jihar RIbas ta kama wani magidanci da zargin cefanar da jaririnsa jim kadan bayan mai dakinsa ta haifa masa shi.

Rahotanni sun ce mutumin da aka bayyana da sunan Mr Izuchukwu Okoye, ya siyar da jaririn a kan Naira dubu dari shida. Sai dai ya fadawa ‘yan uwansa cewa jaririn ya rasu bayan haihuwarsa.

Da take tabbatar da al’amarin, rundunar ‘yan sanda ta hannun kakakinta na jihar Ribas, Nnamdi Omoni ya shaida wa manema labarai cewa al’amarin ya faru a unguwar Igwuruta dake karamar hukumar Obio Akpor ranar wata Lahadi a jihar ta Ribas.

Rundunar ta ce mai dakin mutumin da ake zargi, ta haihu ne a wani gidan siyar da jarirai a unguwar ta Igwuruta, ta ce ta kama masu jami’an karbar haihuwar gidan tare da wanda mutumin da ake zargi.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog