0
Allah Ya yi wa mataimakin-mataimakin shugaban babbar jami’ar Bayero dake Kano, Farfesa Haruna Wakili Haruna
Wasu daga cikin makusantan malamin ne suka bayyanawa DABO FM rasuwar malamin a yau Asabar bayan fama da rashin lafiya.
Kafin rasuwarshi, ya kasance tsohon Darakta a cibiyar Dimokradiyya ta Jami’ar Bayero dake gidan Mumbayya. Tsohon kwamishinan Ilimi a jihar Jigawa.
Ya na daga cikin ‘yan kwamitin da suka gabatar da kirkirar jami’ar Sule Lamido ta Kafin Hausa da kuma jami’ar tarayya ta FUD duk na jihar Jigawa.
