GANDUJE
Labarai Siyasa

An so bawa hammata iska lokacin da Ganduje ke fitar da jagorancin jam’iyyar APC

Tun bayan nasara da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben gwamna da aka gabatar bayan ankai ruwa rana da jam’iyyar adawa ta PDP da dan takarar ta Abba Kabir Yusif, gwamnan ya shiga kokarin gyara musamman a kananan hukumomi na Kano ta tsakiya.

Cikin wani rahoto na DABO FM, Gwamna Ganduje dai ya fara ganawa da masu ruwa da tsaki a kowacce karamar hukuma dake cikin birni da kewaye duba da yanda ba a samu nasara ba, Ganduje ya shiga yi wa jam’iyyar garanbawul.

Ganawar dai na nufin kowacce karamar hukuma ta fitar da jagora guda 1 tal, Majiyar DABO FM ta bayyana cikin irin wannan ganawa ce da masu ruwa da tsakin karamar hukumar Kumbotso, biyu daga cikin jagororin jam’iyyar APC na wannan karamar hukuma suka fara cacar baki, kowanne na ganin shi ne jagoran jam’iyyar.

Daga cacar baka sai aka fara kokarin bawa hammata iska, wanda har sai da takai ga mataimakin gwamnan jihar Kano, Dakta Nasiru Yusif Gawuna, ya tashi domin raba su, nan take gwamna Ganduje yace a kyalesu su dambata.

Daga karshe gwamna ya tsayar da magana akan mai bashi shawara ta fannin siyasa, Mustapha Bakwana, shi ne jagoran jam’iyyar a karamar hukumar Kumbotso maimakon, Wanarabul Manniru Babba Dan Agundi, dan majalisar tarayya na karamar hukumar Kumbotso, abinda shi da magoya bayansa basu ji dadin sa ba.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ganduje ya gwangwaje Zainab Aliyu da Naira Miliyan 3 bayan fitowarta daga hannu Saudiyya

Dabo Online

‘Yan sanda sunyi alkawarin kama duk masu hannu a yiwa Pantami ihun ‘Bamayi’

Muhammad Isma’il Makama

Kano: Ganduje zai biya wa dalibai 38,632 kudin NECO, ya gargadi makarantu akan karbar cin hanci

Dabo Online

Kotun koli ta tabbatar ‘Abba Gida Gida’ a matsayin wanda ya lashe zaben PDP a Kano

Dabo Online

Yanzu-Yanzu: An faɗi gabana ana rokon tilas saina tumɓuke rawanin Sarki Sanusi -Ganduje

Muhammad Isma’il Makama

Kasa da awanni 24 da yin tataburza, Majalissar Kano ta aminta da kudirin Ganduje na karin masarautu 4

Dabo Online
UA-131299779-2