Labarai

Matan kasar Saudiyya sun fara busa sigari a bainar jama’a da sunan samun ‘yanci

Samun ‘yanci a kasar Saudiyya ya sanya an samu karuwar matan da ke busa taba sigari da kuma shisha a bainar jama’a ba tare da fuskantar tsangwama ba.

Majiyar Dabo FM daga kafar RFI ta bayyana daya daga cikin matan Saudiya mai suna Rima ‘yar shekaru 17 da ke aiki a wani kamfani na birnin Riyadh, ta ce, busa sigari a bainar jama’a na cikin ‘yancinta da ta samu a baya-bayan nan.

Rima wadda ta fara zukar sigari shekaru biyu da suka gabata, ta yi watsi da illar da tabar ke yi wa lafiyar bil’adama, amma ta nuna cewa, ba ta son danginta su gano cewa tana shan taba.

Kodayake ta ce, a shirye take ta kare kanta a gaban dangin nata saboda mata na da ‘yancin shan sigari kamar takwarorinsu maza. Masharhanta na danganta hakan da tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa ciki har da bai wa matan ‘yanci da Yarima mai jiran gado Muhammed Bin Salman ke aiwatarwa.

A halin yanzu mata na da ‘yancin tuki da kansu, da halartar filayen wasanni da bukukuwan kalankuwa, da kuma damar yin tafiye-tafiye ba tare da muharraminsu ba, abubuwan da a shekarun baya aka haramta musu

UA-131299779-2