Labarai Siyasa

Wasu da basa son a kau da Boko Haram sun shirya zanga-zangar cire shugabannin tsaro -Garba Shehu

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana wasu mutane dake amfana da rikicin Boko Haram suke zuga ayiwa shuwagabannin tsaro zanga-zanga a ranar Litinin.

Majiyar Dabo FM ta jiyo Garba Shehu na fadin wasu yan siyasa sun yi hayar dubunnan mutane domin yin zanga zangar a fadin Najeriya.

Ya kuma zargi jam’iyyar hayya ta PDP da sanya wa dakarun gwamnatin yekuwa. Yace “mutanen kasar nan na mutukar kaunar gwamnatin Buhari a duk lokacin da suka bi titinan kasar nan.”

“Rahotanni sun ishe mu anyi hayar maza da mata fiye da dubu 2 domin zugawa a cire shugabannin tsaro.”

Daga karshe dai yayi Allah wadai da ihun bamason da akayi wa shugaba Buhari a garin maiduguri, wanda ya zargi jam’iyyar PDP.

Karin Labarai

UA-131299779-2