/

#Op-ed: ‘Karamar hukumar Fagge na fuskantar ƙasƙantaccen wakilci a tarayya’

dakikun karantawa
Aminu Sulaiman Goro
Aminu Sulaiman Goro - Dan Majalissar Tarayyar - Fagge LGA

Ba tun yanzu al’umma suke korafi tare da gunaguni a kan mayaudaran wakilai da suke zaba domin su kare musu hakkokinsu a majalisar tarraya ba, amma har yanzu bata canja zani ba, domin babu gwaggwaban canji da al’umma za tayi alfahari dashi.

Duk wakilin da aka zaba gani yake kamar ya samu tikitin bautar da al’umma ne tare da tara abin duniya ga yayansa da makusantanshi.

Karamar hukumar mu (Fagge), bata tsira daga cikin jerin kananan hukumomin da suke fuskantar kaskantaccen wakilci na yaudara da ha’inci ba, idan mai karatu ya kuduri niyyar nazartar cigaban da wannan karamar hukuma ta samu ta fuskar raya kasa da cigaban unguwa tabbas zai aminta cewa mun fada hannun mummunan wakilci mai cike da yaudara.

Duk wani aikin raya kasa a baki ne babu a aikace, tsawon shekaru goma amma kullum hirar bautar da kwadayayyun yan boko ake da sunan bada gurbin aiki.

Har yanzu babu wani dan asalin karamar hukumarmu (Fagge) da aka samar mishi aikin koyarwa a jami’a sai dai aikin akawu da mai gadi da sauran kaskantattun aikin da ‘ya’yan wannan wakilin tsautsayin baza su yarda suyi ba,  amma a haka ake karade kafafen sada zumunta da karai-rayin ana samarwa matasa aiki.

Idan ka tuhume su a kan cewa wace hanya suke bi gurbin bada aikin tun a nan zaka tabbata da maha’inta ne, balle ka kalli nisan zangon gurin aikin, wannan shi ake kira bautarwa a boye da sunan bada gurbin aiki.

SABON SHAFI A KARAMAR HUKUMAR FAGGE

Umar Aliyu Musa

[email protected]

Karin Labarai

Sabbi daga Blog