/

Rashin Tsaro A Arewa: Buhari da Gwamnonin Arewa sun rasa ikon su a yankin-Ibrahim Garba Umar

dakikun karantawa

Bayan kashe wasu manoma 43 da kungiyar Boko Haram ta yi a Jihar Borno, da kuma wani da aka kai duka kan manoman a Jihar Katsina a kwanan nan, wani shugaban matasa a Zariya ta Jihar Kaduna Hon Ibrahim Garba Umar, yi kira ga ‘yan Arewa da su tashi tsaye su kare kansu daga Boko Haram da ‘yan fashi da kuma masu garkuwa da mutane.
Yana mai cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnonin Arewa sun rasa ikonsu a yankin. An kashe manoman ne a ranar Asabar a Zabarmari, da ke Karamar Hukumar Gere, yayin da masunta da dama suka ji rauni.
Sai kuma wani labari da jaridar Katsina Post ta ruwaito a jiya yake nuna an sake ma wasu manoman kisan gilla a Katsina.

Da yake magana kan lamarin a zantawar sa da manema labarai, ya ce ba za’a sake dogaro da sojojin gwamnati da na tarayya don kare al’ummomin Arewa ba.

Ya kara da cewa Shugaban kasa da sojojin tarayya suna ci gaba da gaya mana cewa suna yin wani abu game da tabarbarewar tsaro, amma ya zuwa yanzu duk ‘yan Arewa dole ne su fahimci cewa an yi watsi da yankinmu saboda halin da ake ciki na tayar da kayar baya wanda ke ci gaba da asarar dukiya mafi girma na Arewa, yawan jama’arta da raunana shi ta fuskar siyasa da kashe shi ta fuskar tattalin arziki.

“Ya isa daukar uzuri da alkawuran karya na aiki daga gwamnatin da har zuwa yanzu ta samu mutuncin zama mafi munin a tarihin kasarmu ta fuskar duk wani karfin da zai samar da kwarin gwiwa wajen cimma tsaron rayukan ‘yan kasa da dukiyoyinsu. “Duk ‘yan Arewa yanzu haka suna cikin fargaba game da karuwar rashin tsaro na al’ummomi da kadarorinsu a Arewa tare da karuwar hare-hare daga ‘yan fashi, barayin shanu da masu tayar da kayar baya, kawai abin da yake cewa mutanen Arewa a yanzu gaba daya suna cikin tarkon kungiyoyin ‘yan bindiga suna yawo garuruwa da kauyuka yadda suke so, suna lalata da barna a cewar Ibrahim Garba Madalla.

Ya ce babu sauran shakku a yanzu cewa gwamnatin mai ci ta Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi sun rasa iko game da wajibcin kare mutanen Arewa, wani aiki ne da tsarin mulki ya rantse wanda suka rantse za su yi, Kuma yanayin yana ta kara ta’azzara a zahiri da rana yayin da ‘yan fashi da masu tayar da kayar baya ke amfani da babban gibin da ake da shi a cikin harkokin siyasa da karfin ikon gudanar da abin da suke amfani da shi tare da mummunan sakamako a kan al’ummomi da daidaikun mutane.

“Mun bayyana a fili abin da ba za a yarda da shi ba ga mutanen Arewa su ci gaba da rayuwa a karkkashin wannan matakin na fadawa ga masu aikata laifuka wadanda ke kai hari, da kashe-kashe, da nakasa, da fyade, da sata, da kona kauyuka da shanun da aka sace, yayin da Shugaban kasa da shugabannin tsaro ke ba da barazanar da alkawuran da basu da wani tasiri.

Kuma yanayin da duk al’ummomin Arewa ke rayuwa a yau ba za a iya jurewa ba kuma dole ne dukkanmu mu tashi tsaye don kare kanmu tare da neman a yi garambawul nan take ga shugabannin sojojin kasar da kuma dukkanin kadarorin tsaro da doka da oda.

Da ya juya ga harin da Kungiyar Boko Haram suka kai a Borno kuwa, Hon Ibrahim Garba Umar ya yi tir da Allah wadai da kisan ta’addanci na rashin imani da rashin hankali da ‘yan ta’addan Boko Haram suka aikata ga wasu manoma a Koshebe da ke kauyen Zabarmari, a karamar hukumar Jere ta Jihar Borno.

Ya na mai cewa a zahirance kisan kiyashin da ake yi a kasar nan ya yi matukar yawa don haka dole a tashi tsaye domin daukan matakai da shawo kan matsalar cikin hanzari.

Ya kuma ce abun kaito ne a ce manoman da suke kokarin samar da abinci ga kasar su ne za a musu yankan rago, “Gaskiya kisan manoman nan abin takaici ne da bakin ciki matuka, a kama su a musu yankan rago a lokacin da suke kokarin ba kawai don su ciyar da iyalansu ba, har ma don su ciyar da kasar mu gaba,Inji Umar

Wannan harin shi ne mafi muni a baya-bayan nan, duka-duka kauye Koshebe da ke karamar hukumar Jere bai wuce tafiyar mintina ashirin da biyar zuwa cikin Maiduguri ba, Amma maka san suka samu damar cin karensu babu babbaka.

Ya tuna da irin bacin ran da ya bayyana a fuskar gwamna Babagana Zulum sa’ilin jana’izar mamatan da aka kashe su 43 tare da dandazon jama’a cikin bakin ciki da alheni, ya lura kan cewa kula da lura shine abu mafi kyawu da jama’a ya kamata su fara nazarta a irin wannan lokacin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog