/

An shiga rudani a Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna

dakikun karantawa

Alamu na nuna cewa Jam’iyyar PDP a karamar hukumar Zariya ta dare biyu tun bayan gudanar da zabukan Shuwagabannin gunduma na Jam’iyyar da aka gudanar a makon da ya gabata.

Hakan ya fito fili ne bayan gangamin ‘ya’yan jam’iyyar da aka kira a yau Lahadi.

Da yake jawabi wurin gangamin taron, jigo a Jam’iyyar PDP a karamar hukumar Zariya Alhaji Ahmed Abdu Zariya Bebejin Zazzau, ya ce tsarin da aka dauka na ‘yaudarar’ ‘ya’yan Jam’iyyar ya saba wa ka’ida da maslahar jam’iyya.

A cewarsa, “kafin gudanar da zabukan da aka yi kwanakin baya, an kira su a uwar jama’iyya ta jiha kuma an tambaye su tsarin da suke so a bi wurin zabo sabbin shuwagabannin jam’iyya a matakin gunduma, kuma duka suka amince a bi tsarin sulhu da dai-daito a bar jagororin da suke kai su zarce, amma daga bisani sai wasu suka shigo da wani nau’in abu na makirci da aka ce an gudanar da zabe.”

Ya kara da cewa; basu yarda da wannan tsari ba kuma ba za su yi biyayya ga wanda aka nada a matsayin jagororin Jam’iyya ba, kuma ba za su sake halartar taron jam’iyya da za a gudanar karkashin jagorancin wancan bangaren ba.

Bebejin Zazzau, ya bukaci uwar jama’iyya ta duba halin da PDP ke ciki a karamar hukumar Zariya, domin hali ne ake ciki na adawa.

A jawabansu daban-daban, Alhaji Ubale Salmanduna da Hajiya Bilkisu Shiba da Alhaji Ishaq Kauran Mata da Kuma Alhaji Magaji Boss, sun nuna rashin amincewarsu kan tsarin da aka bi a jam’iyyar kuma sun ce babu maganar rufa-rufa a jam’iyyar PDP a karamar hukumar Zariya, kuma za su cigaba da sa “kafar wando guda da duk wani mai kawo zagon kasa a jam’iyyar.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog