Manoma 110 aka kashe a Borno – MDD

Karatun minti 1

Majalissar Dinki Duniya ta ce manoma 110 aka yi wa yankan rago a kauyen Zamarmari na jihar Borno.

Mayakan Boko Haram dai ake zargi da aikata ta’addancin a kan manoman da suke girbin shinkafa da safiyar ranar Asabar a jihar karamar hukumar Jere ta jihar Borno.

Majalissar ta ce adadin wadanda aka kashe ya kai 110 tare kuma da samun wasu daga cikinsu da raunuka masu matukar muni.

MDD ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da shugabanta na sashin ayyukan jin kai a Najeriya, Edward Kallon.

Tuni dai aka kammala yi wa manoma 43 da aka yanka sallar jana’iza inda gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum ya halarci sallar.

 

 

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog