(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Rijistaran Kwajelin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano ‘Kano Poly’, Dr Ado ya rasu

Karatun minti 1
Marigayi Dr Ado Muhammad

Dr Ado Muhammad Fagge, Rijistaran Kwalejin Kimiyya da fasaha ta jihar Kano ‘Kano Poly’ ya rasu.
Wani makusancin mamacin ya shaida wa DABO FM cewar Rijistaran kwalejin ya rasu a yau Juma’a a gidansa da ke Unguwar Fagge, cikin birnin jihar Kano.

“Allah Ya yi wa Dr Ado Muhammad, rasuwa yau, za a yi jana’izarsa yau Juma’a a Masallacin Waje da ke Fagge.”

DABO FM ta tabbatar da cewa tini dai babban limamin Masallacin na Waje, Sheikh Muhammad Nasir ya jagorancin yi wa Dr Ado salla bayan kammala Sallar Juma’a a masallacin.

Yayin Sallar Jana’izar Dr Ado Muhammad Fagge

Sai dai har yanzu da muke hada wannan rahoton,  babu sanarwa daga hukumar makarantar.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog