Shugaba Buhari ya yi wa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa

Karatun minti 1
Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kan rasuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.

DABO FM ta tattara cewar tini dai aka binne mahaifin Kwanwkaso a gidan Rabiu Kwankwaso da ke unguwar Bompai a jihar Kano.

Shugaba Buhari ta hannun babban mataimakinsa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana rasuwar mahaifin Kwankwaso a matsayi rashin wani babban jigo da Najeriya ba za ta taba mantawa da irin gudunmawar da bayar ga al’ummar Najeriya ba.

Shugaban ya ce; “Da mutuwar Alhaji Musa Saleh Kwankwaso ta sa mun yi rashin daya daga cikin tsafofafin shugabannin al’umma a Najeriya wanda gudunmawarsa ta tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a matsayin abin da ba za a taba mantawa da shi ba.”

Shugaban ya kara da cewa mahaifin Kwankwaso, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso mutum ne mai nagarta da halaye na gari.

“Ina amfani da wannan dama domin ya mika ta’aziyyata ga tsohon gwamnan Kano Kwankwaso, Gwamnatin jihar Kano da Masarautar Kano biyo bayan mutuwar daya daga cikin shugabanninta. Allah Ya gafarta masa ya kuma saka ayyukansa na gidan Aljanna. Amin.” – Buhari.

Karanta wasu daga labaran mutuwar mahaifin Kwankwaso

Tin daga mukamin Sarkin Kwankwaso zuwa Makaman Karaye, mahaifina ya zauna da mutane lafiya – Kwankwaso

Ganduje ya mika sakon ta’aziyya ga Kwankwaso kan rasuwar mahaifinsa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog