Kai tsaye

Tin daga mukamin Sarkin Kwankwaso zuwa Makaman Karaye, mahaifina ya zauna da mutane lafiya – Kwankwaso

dakikun karantawa
Rabiu Musa Kwankwaso

Kai tsaye: A rika sake loda wannan shafin domin ganin sabbin rahotanni. (Dukkanin magananganun na Rabiu Kwankwaso ne.)

Amsar ko sakon ta’aziyyar Gwamna Ganduje ta iske shi:  Kwankwaso: To gaskiya ni ban ji sakon ta’aziyyar ba, kaga tin da safe da muka fara wannan abubuwan, ban duba waya ba, ban sani ba ko takarda aka kawo.

Amma dan ya yi min ta’aziyya, wannan ba wani abu bane bako dama kuma ya kamata duk wanda yake gwamnan jihar Kano yayi. Idan ma baka yi dan ni ba, ya kamata kayi domin shi.

04: 11 PM: Muna aiki a wannan wajen. Za mu yi wa masallacin nan dori biyu, za a yi Islamiyya da sauran al’amura na addinin Muslunci. Wancen ginin na farko, mun yi shi ne a matsayin asibiti na mata wanda muke sa ran mata za su samu sauki.

Ba dan Korona ba, ta tini kayyakin aikin asibitinma sun shigo. Muna sa rai wannan wajen ma zai zama daga cikin manyan dakunan taro. Sauran guraren ma kai ma (Dan jarida) za ka iya nema a binneka.

04:08 PM: Allah Ya sa kamar yadda kuka gani, mun yi masa kabarinsa a wannan gida (Miller Road).

04:07 PM: A nan nake son gode wa Allah a madadi na da na yan uwa da muka rabu da shi lafiya, har jiya muna tare da shi muna maganganu muna yin abubuwa da yake tsakanin ‘ya’ya da uba. Muna gode wa Allah da ya samu wannan rana ta dacewa ta Juma’a kamar yadda malamai suke fada, muna masa fatan alhairi.

04: 06 PM: Daga wannan matsayi wajen shekaru 20 kenan, daga Sarkin Kwankwaso, Allah Ya sa ya zama Majidadin Kano Hakimin Madobi kuma a wanna rabe-rabe na masarautu har aka ba shi makama Karaye.

04:05 PM: Bana mantawa shekara da aka haife ni 1956, ya zama Sarkin Kwankwaso, tin daga wannan lokaci har yau din nan da muka rabu da shi, duk irin harkar da muke ta siyasa, har zuwa yau din nan ban taba jin wani wanda ya kawo mana wata maganar batanci ko laifi ta bangarensa ba. Ya zauna da mutanensa lafiya tare da dattaku.

04:04 PM: Ina so na yi amfani da wannan dama da yi masa godiya da irin gudunmawar da ya bamu da ni da ‘yan uwa baki daya tin daga ranar da muka zo duniya har zuwa lokacin da ya koma ga Allah.

04:00 PM: Alhamdulillah da rayuwar maji dadin Kano, ya yi rayuwa mai kyau, ya yi rayuwa sama da shekaru 93. Mun gode Aallah da ya bashi damar wanna rayuwar.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog