(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Sa’o’i kadan bayan rantsuwa, Shugaba Buhari zai tafi kasar waje

Karatun minti 1

Shugaba Muhammadu Buhari, zai bar kasa Najeriya, jim kadan bayan sake rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar.

Shugaba Buhari zai halarci taron kungiyar kasashen musulmi “OIC” na duniya karo na 14 a kasar Saudiyya.

Taron zai samu halartar shuwagabannin kasashen da suke membobin kungiyar, za’a gudanar da taron ne ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu, 2019.

Mallam Garba Shehu ya wallafa ta shafinshi na Twitter, inda ya bayyana cewa shugaba Buhari zai bar Najeriya ranar Alhamis, don halartar taron OIC na duniya.

Ana sa ran shugaba Buhari zai yi jawabi akan “Hadin kan membobin kungiyar wajen yakar kalubalen da ake fuskanta” irin na matsalar ta’addanci da fitin-tinu.

Sanarwar tace shugaba Buhari zai dawo ranar 2 ga watan Yuli, 2019.

Daga cikin ‘yan tawagar da zasu raka shugaban akwai gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru ABubakar, Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola da gwamanan jihar Nijer, Abubakar Sani Bello.

Babban sakataren ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje, Amb Mustapha Suleiman, Daraktan hukumar binciken sirri, Amb Ahmad Rufa’i Abubakar, Daraktan cibiyar cigaban harkokin fasaha da kwamfuta, Dr Isa Ali Pantami, shugaban hukumar Alhazai, Abdullahi Mukhtar; suna daga cikin ‘yan raiyar shugaban.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog