0
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya tsallake rijiya da baya, bayan jirgi da ya hau ya kusa yin hatsari a ranar Laraba.
Kamfanin dillancin Labaran Najeriya ”NAN” ya rawaito cewa, jirgin da yake dauke Obasanjo da wasu fasinjojin jirgi 393 a yayin saukarsu a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake jihar Legas.
Jirgin Kamfanin Ethiopian mai lambar, ET-901, ya taso daga filin jirgin saman Bole dake Addis Ababa da misalin karfe 9:10am agogon kasar Habasa (7am agogon Najeriya da Nijar).
