Copyrighted.com Registered & Protected

Ganduje ya fara rabon mukamai

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya fara raba sabbin mukaman jami’an gwamnati da zasu cigaba da tafiyar da mulkin jihar Kano.

Gwamnan ya sake nada sakataren gwamnatin jihar Kano, Usman Alhaji da babban akantan jihar Shehu Mu’azu, domin sake yin aiki dasu a sabon wa’adin gwamnatin da za’a shiga.

Yayi kira da su yi aiki tukuru wajen ciyar da jihar gaba.

Ganduje ya nada su jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar.

Masu alaka

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook
Masu Alaƙa  Buhari ya kira Ganduje zuwa Abuja akan rikicinshi da Sarki Sunusi

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: