Labarai

Sunan ‘Muhammad’ shine sunan da akafi sanya wa jarirai a Birtaniya cikin shekarar 2019

BabyCenter wata hukuma ce ta duniya da take kula da rijistar sunayen da ake sanya wa jarirai musamman a kasashen turawa da sauran manyan kasashen duniya.

A rahoton Dabo FM, BabyCenter ta fitar da wasu alkhaluma na sunaye da aka fi yiwa jarirai rijistar haihuwa dasu a kasashen turai da Amurka.

Alkaluman sun nuna sunan ‘Muhammad’ shine suna mafi shahara da aka fi sanyawa jarirai tare da yi musu rijista a shekarar 2019.

Rahoton kafar yada labaran TheCurrent ta bayya na cewa wannan ai ba sabon abu bane, duba da rahoton kididdigar ta tabbatar da shekara ta 3 kenan a jere sunan yana zama sunan dayafi shahara a fadin Birtaniya.

Haka kuma a shekarar 2014 da 2015 sunan shine wanda aka fi sanyawa a fadin Birtaniya.

Haka kuma a rahoton jaridar TRT ya bayyana akaluman “BabyCenter” dake Amurka sun bayyana cewar sunan Muhammad ya shiga cikin jerin sunaye 10 da aka fi saka wa jarirai maza a 2019 a Amurka.

BabyCenter ta fitar da rahoton shekarar 2019 game da sunayen da ake ba wa yara kanana a Amurka.

Rahoton ya ce a 2019 sunan Liam ne na farko sannan sai Noah,  Aiden, Grayson, Caden, Lucas, Elijah, Oliver da Muhammad ske biyo baya.

Rahoton ya kuma sake fitar da bayanai game da sunan da aka sanyawa yara mata a Amurka a 2019.

An bayyana cewar sunan Aliya na Musulmai ma ya shiga jerin sunayen mata 10na farko da aka fi sanawa jaririai mata a Amurka a 2019.

Alkaluman sun ce sunan Sophia ne na farko inda Olivia, Emma, Ava, Aria, Isabella, Amelia, Mia, Riley da Aliya suka biyo baya.

Karin Labarai

UA-131299779-2