//
Wednesday, April 1

Makarantu a garin Garo dake jihar Kano na cikin halin ko-in-kula

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Garo dai itace mahaifar kwamishin kananan hukumomi Alhaji Murtala Sule Garo, da kuma wasu manya da suka rike madafun iko a Najeriya.

Ƙauyen Alkalawa da ke mazaɓar Garo a cikin ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano, na fama da matsalar rashin ajujuwan makaranta a ƙauyen na su.

Sai dai kuma bayan ‘yar kwarya-kwaryar bincike da Dabo FM tayi, mun gano makarantun wannan gari na cikin halin ko in kula ta ganin yadda dalibai ke daukar darasi a mazaɓar Garo da ke jihar Kano.

Ilimin Furamare na ƙara samun koma baya a wasu daga ƙananan hukumomin jihar Kano duk da kuɗaɗen da gwamnatoci ke warewa fannin na ilimi.

Masu Alaƙa  Zaben Gwamna: Wasu fusatattun matasa sun kone mota cike da dangwalallun kuri'u a Kano

Ƙarancin kujerun zama da kayan aiki na koyo da koyarwa na ci gaba da kassara karatun ‘ya’yan talakawa a waɗannan ƙananan hukumomi.

Matsalar rashin ajujuwan ta sanya al’ummar wannan ƙauye yin amfani da karan Masara da na Gero wajen yin rumfar da ƴaƴansu za su dauki darasi a ciki.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020