Labarai

Nan da shekaru 2, Najeriya zata fara fitar da Shinkafa zuwa kasashen waje – Sabo Nanono

Nanono Ministan aikin goba da raya karkaka Alhaji Sabo Nanono ya bayyana cewar nan da shekaru biyu kacal masu zuwa, Najeriya za ta fara futar da Shinkafa zuwa kasashen waje don siyarwa bayan ta wadaci kasa.

Nanono wanda yake tare da Ministan yada labari da al’adu, Alhaji Lai Mohammad, a lokacin da suka ziyarci karamar hukumar Kura ta jihar Kano, don ganin tasirin da rufe iyakar Najeriya ta tudu don haramta shigo da Shinkafa yayi, ya bayyana gamsuwa da kuma jin dadin yanda noman Shinkafar yake bunkasa a yankin.

. A lokacin wannan bincike, ministicon sun kai ziyara wasu masana’antun sarrafa shinkafa a yankin da suka hada da Tiami Rice ltd, Kura brothers rice mill, da Hamsad Rice da dai sauransu.

Tun da farko da yake yin godiya gami da nuna goyon baya ga ziyarar, shugaban masu sarrafa da siyar da shinkafa a Kura, Alhaji Ali Idris, ya jaddada fatansa ga gwamnati na ganin an ci gaba da rufe iyakokin kasar.

Domin Najeriya za ta iya ciyar da mutanenta ta noma kayan abinci masu yawa, da sau da dama ake safararsu zuwa kudancin kasar.

UA-131299779-2