Shugaban sojin sama ya yi ‘wuff’ da Ministar Jinƙai, Sadiya Umar Faruq

Karatun minti 1

Shugaban sojin sama na kasa, Air Marshal Sadique Abubakar ya angonce da Ministar walwala da jinƙai ta Najeriya, Sadiya Umar Farouq.

Wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar wa Dabo FM cewa an daura auren ne ranar 18 ga Satumba a masallacin Juma’a na Maitama dake babban birnin tarayya, Abuja.

Kamar yadda aka sanar da mu cewa “Kwarai gaskiya ne shugaban sojin sama ya angonce da ministar jinƙai.” a ta bakin daya daga cikin majiyarmu.

“Mutane kadan aka gayyata wajen daurin auren saboda ma’auratan basa so duniya ta sani.”

Wata majiyar tamu ta bayyana ma’auratan sun jima suna soyayya da junan su kafin a daura auren.

“Sun jima suna soyyaya, daurin auren ya kawo karshen jita jitan da ake na akwai alaƙa tsakanin minista da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.” Kamar yadda DailyTrust ta fitar.

Rahotannin sun bayyana shugaba Buhari ya auri ministar a Oktobar 2019, wanda ya jawo cece-kuce, daga karshe fadar shugaban ƙasa ta magantu, tare da ƙaryata jita jitan.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog