/

Godwin Obaseki na PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Edo

Karatun minti 1
Godwin-Obaseki- Gwamnan Edo

Dan takarar gwamna jihar Edo a jami’iyyar PDP, Godwin Obaseki ya lashe zaben gwamnan jihar a karo na biyu.

Hukumar zabe ta INEC ce ta sanar da haka da ranar yau bayan kammala tattara sakamakon zaben da aka gudanar a karshen makon nan.

Godwin Obaseki ya samu kuri’u 307,955, tare da samun nasara a kananan hukumomi 13 daga 18 na jihar.

Godwin-Obaseki- Gwamnan Edo

Dan takarar APC, Fasto Osagie Iza Iyamu ya samu kuri’u 223,619 tare da samun nasara a kananan hukumomin jihar guda 5 kacal.

An samu tsiran 84,336 tsakanin ‘yan takarkarun guda biyu, adadin da ya fi na kuri’un da aka soke

Karin Labarai

Sabbi daga Blog