Tallafin Korona: Gwamna ya raba tumatirin leda, taliyar yara guda bibbiyu

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Ebonyi ta kaddamar da bada tallafin kawar da radadin da cutar Koronabairas ta haddasa a fadin jihar baki daya.

DABO FM ta tattara cewa an bayar da tallafin ne a matakin akwatin kada kuri’a, wanda aka fara da makarantar sakandare ta Amuzu Community dake karamar hukumar Ezza Ta Kudu.

Majiyar mu ta bayyana mataimakin gwamnan jihar, Dr.Kelechi Igwe shi ne ya jagoranci gagarumin taron bada tallafin, duk da dai an so a samu tangarda wajen yin rabon.

Bayan dakatar da rabon, sakataren gwamnatin jihar Ebonyi ya bayyana cewa “Dalilin dakatar da rabon ya biyo bayan wasu bata-gari da suka yi shirin kwace kayan daga hannun hukuma, za a cigaba washe gari.”

Wani da ya karbin tallafin

Wakilinmu ya bayyana mana cewa cikin abubuwan da aka raba akwai ledar taliyar Indomie guda biyu, Tumatirin leda guda 1, shinkafa mai nauyin 5kg, rabin kwalin sikari, man girki 50cl ga kowanne magidanci.

Rabon zai ci gaba ranar Lahadi a mazabun sanatoci guda 2. Kamar yadda DailyTrust ta fitar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog