Shugaban Daliban jihar Bauchi, Adamu Kaloma ya shaki iskar ‘yanci

Karatun minti 1
Adamu Musa Kaloma - Shugaban NUBASS

Rahotannin da suke iske DABO FM sun tabbatar da cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi sun saki shugaban daliban jihar Bauchi, Adamu Musa Kaloma.

Hakan na zuwan awanni kadan bayan da jami’an tsaro suka kama matashin sakamakon yunkurin hada zanga-zanga neman sahalewar gwamnatin jihar Bauchi da ta bude makarantu tare da biyan wasu daga cikin daliban jihar hakkokinsu na tallafi daga gwamnatin.

Da yake tabbatarwa da a shafinsa na Facebook, Kaloma ya ce ya shaki iskar ‘yanci, sai dai ya bayyana cewar rashin ganin nashi ba shi da alaka da gwamnati ko jami’an tsaro, ya kuma ce zai bayyana yadda ta kasance bada dadewa ba.

Sai dai ana zargin an yi masa barazanar bayyana hakikanin abinda ya faru da shi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog