Ana cigaba da jimamin mutuwar Ganiyyu Abdulrazaq, Lauyan Arewa na farko

Karatun minti 1
Marigayi Ganiyyu Abdulrazak -SAN

A daren ranar Juma’a, 3 ga watan Dhul Qadah 1441 – 23/7/2020, lauyan farko a yankin arewacin Najeriya, Ganiyu Folorunsho AbdulRazaq, ya rasu a babban birnin tarayyar Najeriya dake Abuja.

Ya rasu yana da shekara 93 a duniya. Kafin rasuwarshi ya kasance tsohon Minista mai kula da jiragen kasa a jamhuriyar Najeriya ta farko.

Iyalan mamacin ne suka sanar da mutuwarshi a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alimi Abdulrazaq.

“Tare da sallamawa Allah Madaukakin Sarki, mu iyalan AbdulRazak na masarautar Ilorin na jihar Kwara muna sanar da rasuwar Alhaji AbdulGaniyu Folorunsho Abdul-Razak SAN (OFR), ya rasu yana da shekara 93 a Abuja. An haifeshi a shekara ta 1927.”

Ya kasance mai rike da sarautar Mutawalin Ilori da Tafidan Zazzau. Kazalika shugaban Nigerian Body of Benchers.

Ya rasu ya bar matarshi, Hajiya Raliyat Abdulrazaq mai shekaru 90, tare da ‘ya’ya da jikoki, daga cikinsu akwai gwamnan jihar Kwara na yanzu, Abdurrahman Abdulrazaq.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog