(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Taraba: Kungiyar ASUU ta kara tafiya yajin aikin sai baba ta gani

Karatun minti 1

Kungiyar ASUU, reshen jihar jami’ar jihar Taraba ta sake komawa yajin aikin sai baba ta gani a yau Laraba, 03/04/2019.

Kungiyar dai ta cigaba da yajin aikin ne bisa rashin cika alkawarin gwamnatin jihar tin bayan wata matsaya da bangarorin biyu suka cimma a shekarar data gabata.

Gabannin karshen shekarar 2018 kungiyar ta dakatar da yajin aikin data dauka bayan cimma matsaya tsakaninta da gwamnatin jihar ta Taraba.

Daga cikin alkawuran da gwamnatin jihar ta gaza cikawa, sun hadar da rashin biyan kudin alawus da  ‘yayan ASUU suke bin gwamnatin tin daga shekarar 2014 zuwa yanzu, tare da rashin kammala wasu gine-gine a cikin makarantar.

Da yake jawabi Dr. Samuel Shikaa, shugaban  kungiyar ASSU reshen jihar jami’ar jihar, yace ‘yayan kungiyar zasuyi zamansu a gida har sai gwamnatin ta aiwata da alkawuran data dauka.

Kungiyar ta kara da cewa, gwamnati ta karya dokar tarawa makarantar kudaden gudanarwa, dokar data bawa makarantar damar samun kudade daga gwamnatin jihar dama ta kananan hukumomi.

“Idan aka zagaya cikin makarantar nan, za’a ga ginin da gwamnati ta  fara amma ta gaza karasawa, duk ginin da yake a kammale, to lallai hukumar TET Fund ce tayi shi. Shiyasa idan kace makarantar nan mallakin TET Fund ce, to tabbas ba’a aikata laifi ba.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog