0
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i ya jagoranci tawagar jami’an tsaro wajen fatattakar masu garkuwa da mutane a kan tituna.
A cikin makonnan dai aka samu rahotanni dake nuni da wasu guggan masu garkuwa da mutane sukayi tsaiko tsaiko akan titin Kaduna-Abuja suna tare mutane tare dayi musu fashi da kuma yin garkuwa dasu.
A kalla mutane da dama ne suka bata dalilin dauke su da masu garkuwar sukayi.
Babban mataimakin Gwamna El-Rufa’i a fanni labarai, Samuel Arawun, ya tabbatar da tarwatsa bata garin da gwamnan ya jagoranta a yau Laraba.
Kalli hotuna:

